Rahotanni daga Najeriya na cewa gwamnan jihar Zamfara Abdulaziz Yari, ya ce a shirye yake ya sauka a kujerarsa domin a ayyana dokar ta baci a jihar, idan har matakin zai magance matsalar tsaro da ta addabi jihar.
Jaridun Najeriya da dama sun ruwaito cewa, Yari ya bayyanawa manema labarai hakan ne yayin da ake ta sukar hukumomi kan kin daukan matakan maganace matsalar tsaro a jihar, lamarin da ya kai ga aka yi wata mummunar zanga zanga makonni biyu da suka gabata a yankin Tsafe.
A cewar Yari, wanda har ila yau shi ne shugaban kungiyar gwamnonin Najeriya, idan akwai jami'an tsaro, batun masu satar mutane, 'yan bindiga da 'yan ta'adda zai zama labari, kamar yadda jaridar Vanguard ta wallafa a shafinta na yanar gizo.
Zamfara ta jima tana fama da matsalar ‘yan bindiga wadanda kan kai hare-hare akan mutanen da ba su ji ba ba su gani ba.
Wannan matsala ta raba dubban mutane da muhallansu inda suke zaune a sasanonin ‘yan gudun hijira a sassan jihar da ma makwabciyarta ta Katsina.
A kwanakin baya, hukumomin Najeriya sun kaddamar da wani shirin magance harin ‘yan bindigar mai taken “Operation Dirar Mikiya,” ko da yake, wasu na cewa shirin ba ya tasiri.
Amma jami’an tsaro a ‘yan kwanakin nan sun bayyana nasarar tarwatsa maharan da dama a wasu yankunan jihar.