Accessibility links

Dambarwar siyasar jihar Taraba ta dauki wani salo daban

Dambarwar siyasar jihar Taraba ta dauki wani salo daban. Tun lokacin da gwamnan jihar Danbaba Suntai ya samu hatsari a jirgin saman da shi da kansa yake tukawa kusan watanni shida da suka gabata jihar ta shiga halin kakanikayi.

Kawunan mutane sun rabu. Wasu na son a rantsar da mataimakin gwamnan ya zama mai cikkaken iko yayin da wasu kuma suka ki amincewa. Wasu ma har sun garzaya kotu suna neman a tilastawa yan majalisar su yadda a rantsar da mataimakin gwamnan

Jiya sai ga shi majalisar ta tsige duk shugabanninta ta zabi wasu sabbi. Bayan zaben cecekuce ya taso inda a ke zargi mataimakin gwamnan da Sanato Aisha Alhassan da hannun a lamarin. Yayin da Sanato Ibrahim Goje ya kare mataimakin gwamnan ita ko cewa ta yi ita ba yar majalisar jihar ba ce.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG