Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Bindiga Ya Bude Wuta Akan Yahudawa a Amurka

Wurin ibadar da aka kai hari a birnin Poway na kasar Amurka, ranar 27, Afrilu 2019.
Wurin ibadar da aka kai hari a birnin Poway na kasar Amurka, ranar 27, Afrilu 2019.

Babban jami’in dan sandan ya ce, wani dan sanda da ya tashi a aiki, ya hango dan bindigar yana tserewa daga wurin ibadar bayan aikata wannan mummunan aiki, har ma ya harba bindigarsa, amma bai same shi ba.

Akalla mutum daya ne ya mutu a Amurka, bayan da wani dan bindiga ya shiga wani wurin ibadar Yahudawa a birnin Poway da ke Jihar California ya bude wuta.

A lokacin wani taron manema labarai, shugaban ‘yan sandan San Diego, Bill Gore, ya ce, wani mutum farar fata, ya shiga wurin ibadar da misalin karfe 11:30 na ranar jiya Asabar, ya bude wuta da bindiga kirar AR.

Ya kuma raunata mutum hudu, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar mutum daya daga cikin mutanen hudu.

Babban jami’in dan sandan ya ce, wani dan sanda da ya tashi a aiki, ya hango dan bindigar yana tserewa daga wurin ibadar bayan aikata wannan mummunan aiki, har ma ya harba bindigarsa, amma bai same shi ba.

Amma daga karshe, dan bindigar, mai shekaru 19, ya tuntubi ‘yan sandan San Diego ya kuma mika kansa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG