Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake A Iraqi Ya Kashe Mutane 14


Nigeria Violence

Jiya Lahadi a Iraqi, wani dan kunar bakin wake ya kashe akalla mutane 14, a wani sansanin 'yan gudun hijira da tashe tashen hankula a cikin kasr suka raba su da muhallansu.

Haka nan harin ya jikkata wasu mutum 13, a sansanin mai tazarar kilomita 60 yamma da Ramadi, babban birnin lardin Anbar.
Nan da nan babu wanda ya fito ya dauki alhakin kai harin.
Dakarun Iraqi sun kwato biranen Ramadi da Fallujah daga hanun mayakan sakai na kunigyar ISIS, amma mayakan sakan masu ikirarin jihadi suna ci gaba da iko da yammacin lardin.
A can kasar Syria kuma,, tashar talabijin ta kasar ta bada rahoton cewa wani dan harin kunar bakin wake ya tarwatsa kansa a dandalin Tahriri dake tsakiyar birnin Damascus jiya Lahadi, ya halaka akalla mutane goma sha takwas ya jikkata wasu mutane masu yawa.
Kungiyar dake nazarin kare hakkin Bil'Adama a Syria ta bayyana harin a zaman daya daga cikin hare hare guda uku da aka boye bamai bamai cikin mota da suka tashi.
Jami'an tsaron kasar suka ce, sun koro 'yan harin kunar bakin uku cikin motoci, suka halaka biyu a kofar shiga birnin kamin su yi barna. Vidiyon talabijin ya nuna akalla motoci biyu da suka kone kurmus da wasu baraguzai akan hanyar zuwa tashar jirgin sama na kasar.
Matuki na uku ya bacewa hukumomin tsaro, amma daga bisani ya tarwatsa kansa a dandalin na Tahrir bayan da aka yi masa zobe.

Facebook Forum

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG