Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Kunar Bakin Wake Dauke Da Kwando


Kunar Bakin Wake
Kunar Bakin Wake

A yayinda jama'a ke ta farinciki da sa ran cewar sabuwar gwamnatin da aka rantsar zata share masu hawaye musamman ta fannin harkar tsaro, wani dan kunar Bakin Wake ya shiga kasuwar kwata a jahar Maiduguri.

Rahotanni na nuna cewar yau da misalin karfe goma sha biyu na rana wani dan kunar Bakin Wake ya shiga wata kasuwa da ake kira kwata cikin garin Maiduguri inda ake yankan dabbobi, kuma ana smun cinkoson jama'a sosai a wanna kasuwa musamman mahauta da ke zuwa sarin nama.

kamar yadda rahoton ya bayyana, dan kunar bakin waken ya shiga kasuwar ne dauke da wani kwando a hannun sa wanda jama'a suka yi tunanin kamar mai tallar magani ne a yayin da yake tafiya cikin kasuwar koda shike ba'a farga da abin da ke cikin kwandon ba.

Dan kunar bakin waken ya tafi har zuwa tsakiyar kasuwar sa'an nan ya tada bam din da yake dauke da shi wanda ya hallaka mutane da dama, saidai kawo yanzu ba'a sami wani cikakken bayanin da ya bayyana adadin yawan mutanen da bam din ya hallaka ba.

Hare haren kunar bakin wake dai tamkar ruwan dare ne gama duniya a wannan yanki ko da shike an sami saukin su daga baya amma da alamun sun fara cigaba da shiga wurare suna kai hare haren.

Rahotanni na nuna cewar kusan mako guda kenan ana samun hare hare makamantan wannan, kamar yadda wani dan kunar Bakin waken ya hallaka kansa da kansa a garin Biu wanda shima yayi yunkurin kutsawa cikin jama'a ne amma bai sami damar hakan ba har bam din ya hallaka shi.

Dan Kunar Bakin Wake Dauke Da Kwando - 2'57"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG