Accessibility links

Bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita, fitaccen mawakin Hausa nan da aka fi sani da Dan Maraya Jos ya rasu.

Rahotanni daga Jos, babban birnin Jahar Filaton Najeriya na cewa shahararen mawakin nan na Hausa Dan Maraya Jos ya rasu.

Dan Maraya ya rasu ne ya na mai shekaru 69 bayan fama da ya yi da rashin lafiya na wani tsawon lokaci.

An haife shi ne a garin Bukuru da ke Jos ta Kudu a shekarar 1946.

Cikakken sunansa shi ne Alhaji Adamu Dan Maraya Jos, ya kuma samu inkiyar “Dan Maraya” ne bayan rasuwar mahaifansa a lokacin ya na jariri.

Marigayin ya yi fice ne a wakokinsa ta hanyar amfani da Kuntigi, wata ‘yar karamar jita mai layin zare daya, wacce ba ya rabuwa da ita.

Daga cikin fitattun wakokinsa da suka sa ya yi fice akwai wakar “Karen Mota” da “Gulma Wuya” da “ A Daina Shan Kwaya” da “Talaka” da dai sauransu.

Ba kamar sauran mawaka ba, wakokin Dan Maraya sun fi karkata ne wajen nuna matsalolin rayuwa, zamantakewa, shugabanci da yin nasiha musamman ga matasa da kuma zaman lafiya da wa'azi.

Ga karin bayani a rahoton Zainab Babaji daga Jos:

XS
SM
MD
LG