Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Sanda Ya Rasa Ransa a Wani Harin Bam a Jihar Rivers


Wasu 'yan sandan Najeriya ke nan a wurin atisaye.

Yayin da ake kokarin inganta matakan tsaro a Najeriya saboda zabe mai gabatowa sai ga shi wani harin bam ya halaka wani dan sanda tare da raunata wasu da dama a Jihar Rivers.

Dan sanda guda ya rasa ransa a Jihar Rivers bayan da aka kai wani hari a lokacin yakin neman zaman dan takarar gwamna a karkashin jam’iyar APC.

Wakilin VOA ya ruwaito cewa wasu da dama sun sami rauni a harin ciki har da wani dan jarida.

Bam din ya tashi ne yayin da dan takarar gwamna na jam’iyar APC Dr. Dokuku Peter Saye ya ke gudanar da gangamin yakin neman zabe a makarantar sakandare ta Okirika dake jihar.

Rahotanni sun ce an ji harbe-harbe bayan da bam din ya tashi lamarin da ya sa mutane suka bazama domin neman mafaka.

Najeriya dai na tunkarar babban zabe a ranar 28 ga wannan wata na Maris inda jami'ya mai mulki ta PDP ke fuskantar kalubale daga babbar jami'iyar adawa ta APC.

An dage zaben ne daga ranar 14 ga watan Fabrairun da ya gabata bayan da jami'an tsaron kasar su ka ce ba za su iya samar da kariya a zaben ba har sai an musu karin lokaci.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG