Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Adamawa: 'Yan Gudun Hijra na Shirye-Shiryen Zabe


Wani Sansanin 'yan gudun Hijra a arewa maso gabashin Najeriya.

Bayan kwato wasu yankuna daga hanun 'yan kungiyar Boko Haram 'yan gudun Hijra da dama a Jihar Adamawa na komawa gida domin tunkarar zabe.

‘Yan gudun hijra da rikicin Boko Haram ya raba da muhallansu a jihar Adamawa sun fara komawa gidajensu sun kuma ce a suna shirye-shiryen tunkarar zabukan da za a gudanar.

Rahotanni na nuni da cewa ya zuwa yanzu jami’an tsaro sun kwato kusan daukancin garuruwan da ke hannun masu ta da kayar baya, lamarin da ya baiwa ‘yan gudun hijra da yawa damar komawa gidajensu.

“Yanzu ya kamata hukumar zabe ta shirya ta san yadda za ta je ta shiga inda za a yi zabuka.” In ji Emmanuel Face, wani mazaunin jihar ta Adamawa.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG