Accessibility links

Dan Sanda Ya Rasa Ransa Sanadiyar Rikicin Mallakar Gona a Jihar Gombe

  • Grace Alheri Abdu

wadansu gidaje da kungiyar Boko Haram ta lalata

Rahotanni daga jihar Gombe na nuni da cewa, wani jami’in dan sanda ya rasa ransa sanadiyar rikicin mallakar gona tsakanin al’ummomin kananan hukumomin Billiri da kuma Shongom.

Kakakin hukumar yan sanda a jihar Gombe DSP Obed Mary Malum ta shaida haka a hirarsu da Sashen Hausa, ta kuma bayyana cewa, kwamishinan yan sanda ya tura jami’ai a yankunan biyu domin kwantar da hankula.

Ta bayyana cewa an kona gidaje sha bakwai a garin Kufayi, banda haka kuma a kashe daya daga cikin jami’an ‘yan sandan da aka tura domin kwantar da tarzomar. Bisa ga cewarta, rikicin ya sami asali ne tun kaka da kakanni.

Ga cikakken rahoton da wakilinmu Abdulwahab Mohammed ya aiko mana

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG