Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan sandan Turkiya Ya Harbe Jakadan Rasha Na Turkiyan


Andrey Karlov, jakadan Rasha ya fadi kasa a birnin Ankara yayinda dan bindigan ya harbeshi
Andrey Karlov, jakadan Rasha ya fadi kasa a birnin Ankara yayinda dan bindigan ya harbeshi

A jiya wani Dan-sandan Turkiyya, da ba ya akan aiki, ya harbe Jakadan Rasha a birnin Ankara, kuma dukkan alamu na nuna cewa ya aikata danyen aikin ne don bayyana haushinsa kan rawar da Rasha ke takawa a yakin kasar Syria.

An dai kai farmakin ne a daidai lokacinda Jakada Andrey Karlov yake jawabi a wajen wani shagalin nunin fasahun zane-zane.

A cikin faifan bidiyo da aka nuna na farmakin, an ga matashin da yayi harbin tsaye bayan jakadan, abinda yassa wasu suka dauka cewa shi dogarinsa ne.

Lokacinda yayi harbin, matashin yayi ta kabarra “Allahu Akbar, Allahu Akbar”, yayinda yake rantsuwar cewa sai sun rama abinda ya kira “kashe-kashen gilla” da Rasha ke yi wa mutanen Syria.

Wani daga cikin mutanen da suka shedi al’amarin ya gayawa gidan rediyon nan na Muryar Amurka cewa ya ji maharbin yana cewa, “Kada ku manta Aleppo, kada ku manta da Syria. Muddin kasarmu ba ta zauna lafiya ba, ku ma ba zaku zauna lafiya ba!” Magajin garin birnin na Ankra, Melih Gokcek, ya ce sunan Dan-sandan da yayi harbin shine Melvut Mert Altintas, mai shekaru 22.

Danbindigan da ya hallaka jakadan Rasha jiya Disamba 19, 2016.
Danbindigan da ya hallaka jakadan Rasha jiya Disamba 19, 2016.

Tuni dai shugaban Rasha, Vladimir Putin, ya la’anci harin.

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG