Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Shekara 30 Ya Lalata 'Yar Makwabcinsa Mai Shekara 2 Da Haihuwa


Fyade: Say No To Rape

Wata babbar kotun jihar Adamawa da ke Yola, ta ba da umarnin tsare wani mutum mai shekaru 30, bisa zargin yi wa yarinya ‘yar shekara 2 da haihuwa fyade.

Ana zargin mutumin mai suna Ali Ibrahim da lalata yarinyar ‘yar shekara 2 ne a cikin gidansa da ke unguwar Kwacham, a cikin yankin karamar hukumar mulkin Mubi.

Rahotanni sun bayyana cewa wanda ake zargi ya yaudari yarinyar wadda ‘yar makwabcinsa ce zuwa cikin dakinsa, inda ya yi lalata da ita.

Ali wanda ke sana’ar sayar da itacen girki, ya amsa cewa ya shigar da yarintar a dakinsa, ya kwantar da ita a kan gado ya kuma yi lalata da ita.

Ya fadawa alkalin babbar kotun ta 2 a Jimeta cewa, bayan aikata laifin, ya raka yarinyar har zuwa gidansu, inda nan take mahaifiyar ta ta gano wani bakon al’amari a jikinta.

Ya ce daga bisani uwar ce ta kai rahoton ga ‘yan sanda, inda nan take suka kama shi suka kuma gurfanar da shi a gaban kotu.

Alkalin kotun, Mai Shari’a Helen Hammajoda, ta dage sauraren karar zuwa ranar 27 ga watan nan na Oktoba, kana kuma ta ba da umarnin a ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali na Yola kafin zuwan ranar.

XS
SM
MD
LG