Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Shugaban Kasar Equatorial Guinea Yayi Odan Jirgin Ruwan Alatu Kan Kudi Naira Milyan Dubu 57


Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasongo na kasar Equatorial Guinea.

Kungiyar Global Witness mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, ta ce wani dan shugaban kasar Equatorial Guinea inda jama’a ke fama da talauci, yayi odar wani jirgin ruwan alatu na alfarma a kan zunzurutun kudi dala miliyan 380, kimanin Naira miliyan dubu 57.

Kungiyar Global Witness mai yaki da cin hanci da rashawa a duniya, ta ce wani dan shugaban kasar Equatorial Guinea inda jama’a ke fama da talauci, yayi odar wani jirgin ruwan alatu na alfarma a kan zunzurutun kudi dala miliyan 380, kimanin Naira miliyan dubu 57.

Wani binciken da kungiyar Global Witness ta gudanar ya nuna cewa jirgin ruwan alatun da dan shugaban yayi oda tana dauke da wurin ninkaya, da gidan sinima, da gidan abinci, da kuma na’urorin tsaro na dala miliyan daya, kimanin Naira miliyan 150.

An yi odar wannan jirgin ne daga wani kamfanin kasar Jamus mai suna Kusch. Teodorin Obiang da ne na shugaba Toedoro Obiang na kasar Equatorial Guinea. Kasar dake Afirka ta yamma tana da arzikin man fetur, amma akasarin al’ummar kasar su na zaune cikin bakin talauci, yayin da ake tattake musu hakki.

Ma’aikatar shari’a ta Amurka, wadda ta binciki ajiye-ajiyen Obiang a bankunan Amurka, ta zargi gwamnatin kasar da laifin wawurar kudaden jama’a tare da yin magudin zabe.

Global Witness ta ce dan na shugaba Obiang yana da gida na dala miliyan 35 (Kimanin Naira miliyan dubu 5 da 250) a Jihar California a nan Amurka, da wasu motoci na alfarma, da jirgin sama na kashin kansa, duk da cewa albashinsa bai taka kara ya karya ba a matsayinsa na ministan ayyukan gona a Equatorial Guinea.

Jami’an gwamnatin Equatorial Guinea sun tabbatar da cewa lallai Teodorin yayi odar wannan jirgin ruwa, amma daga baya ya fasa saye.Jami’an suka ce yayi niyyar biyan wannan jirgin ruwa ne daga kudaden da yake samu a harkokin kasuwancinsa, ba wai da kudin gwamnati ba.

XS
SM
MD
LG