Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Dan Tagwayena Ya Rasu,' -Ronaldo


Cristiano Ronaldo

"Dan Tagwaye Na Ya Rasu "- Cristiano Ronaldo

Cristiano Ronaldo ya yi amfani da shafukan sada zumunta a jiya Litinin wajen bayyana cewa daya daga cikin tagwayen da aka haifa masa ya mutu.

"A cikin yanayi na bakin ciki ya kasance dole mu sanar da cewa dan jinjirinmu ya rasu," in ji dan wasan na Manchester United a wani sakon da abokin aikinsa, Georgina Rodriguez, ya sanya wa hannu.

Ya kara da cewa, "Wannan shi ne yanayi mafi ciwo da duk iyaye za su iya ji." Ronaldo ya sanar a bara cewa shi da matarsa su na kyautata zaton za su haifi tagwaye.

"Haihuwar 'yar mu ce kawai ke karfafa ma na rayuwa a wannan lokacin tare da kyakkyawan fata da farin ciki," abin da ya rubuta kenan a shafin sada zumunta na yanar gizo. Sanarwar ta kara da cewa, "Dukkanmu mun kadu da wannan rashi, kuma muna neman kadaicewa a cikin wannan mawuyacin lokaci. Danmu, kai ne abun kaunar mu. Za mu cigaba da kaunarka a koyaushe."

Ronaldo yana da 'ya'ya hudu a yanzu haka.

- MANCHESTER, England (AP)

Kofin Duniya ta Qatar 2022

Kofin Duniya ta Qatar 2022
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:32 0:00
Karin bayani akan Kofin Duniya ta Qatar 2022

Ronaldo vs. Messi

Ronaldo vs. Messi
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:24 0:00
Satumba 30, 2020

Ronaldo vs. Messi

Karin bayani akan Wasanni
XS
SM
MD
LG