Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dan Takarar Jam Iyyar Hamayyar Najeriya Na Da Ja Game Da Sakamakaon Zaben Shugaban Kasar


Kone-konen da su ka wakana bayan sakamakon zaben da ya ballo da tarzoma a duk arewacin kasar Najeriya

Dan Takarar Shugaban Kasar Najeriya Da Bai Yi Nasara Ba Ya Na Ci Gaba da Gardama Akan Sahihancin Zabe.

Dan takarar shugaban kasar Najeriya da bai yi nasara ba Muhammadu Buhari na ci gaba da kin yarda da sahihancin zaben, a lokaci guda kuma ya na yin kira cewa a kwantar da hankula bayan munanan tashe-tashen hankulan tarzomar da aka yi a arewacin kasar.

Mr.Buhari ya gayawa Sashen Hausa na Muryar Amurka a yau Laraba cewa ba a yi zabe a yankin Niger Delta ba da kuma yankin kudu maso gabashin kasar, sannan ya ce an hana magoya bayan shi yin zabe a yankunan. Amma ya yi kira ga jama'a a kwantar da hankula a bi doka, ya ce su da hukumar zabe na bin kadun duka abubuwan da aka yi ba daidai ba.

Shugaban kasar Najeriya Goodluck Jonathan ya lashe zaben ranar asabar, wanda 'yan kallo masu zaman kan su, su ka ce yawanci ya gudana cikin gaskiya da adalci.

Tarzoma ta barke a arewacin kasar bayan da Mr.Jonathan ya yi galaba a kan Mr.Muhammadu Buhari.

Shaidu sun tabbatar da cewa sun ga gawarwakin mutane a kone kurmus a yaryashe a kwararo, kuma an kona gidaje da Majami'u su ma kurmus.

Matasa masu tarzomar kin yarda da sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya
Matasa masu tarzomar kin yarda da sakamakon zaben shugaban kasar Najeriya

Kafofin yada labarai sun ce watakila mutane kamar hamsin (50) ne su ka mutu a cikin tashin hankalin, duk da cewa jami'an gwamnati da kungiyoyin agajin jin kai sun ki bayyana alkaluman mace-mace don gudun kar hakan ya sake janyo barkewar hare-haren ramuwar gayya.

Babu jam'iyyar hamayyar da ta sanya hannu akan takaradun amincewa da sakamakon zabe na karshe sannan kuma jam'iyyar Mr.Buhari ta kalubalanci sakamakon ta hanyar da ta kamata.

Jami'ai sun ce Mr. Jonathan ya samu kuri'u fiye da miliyan ishirin da biyu (22,495,187) a zaben ranar asabar, kusan ninkin ba ninkin kuri'un da Mr.Buhari ya samu wadanda jami'an zabe su ka ce sun kai miliyan goma sha biyu da 'yan ka (12,214, 853).

Shugaba Goodluck Jonathan na karban 'yan taya murna bayan da jami'an hukumar zabe su ka ce ya lashe zaben shugaban kasar na ranar asabar.
Shugaba Goodluck Jonathan na karban 'yan taya murna bayan da jami'an hukumar zabe su ka ce ya lashe zaben shugaban kasar na ranar asabar.

Mr.Jonathan ya samu isasshen goyon bayan da ya hana yin zagaye na biyu, ya samu kashi 57 cikin dari na kuri'un da aka kada.

Najeriya wadda ta fi kasashen Afirka yawan jama'a, ta na da mutane miliyan dari da arba'in (140,000,000) da su ka kunshi Musulmi da Kirista. Akasarin Musulmin kasar su na arewa, su kuma Kirista mafiya yawa su na kudu.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG