Accessibility links

Dandalin Gwamnonin Najeriya ya nemi goyon bayan kungiyoyin mata a yaki da cutar Polio


An nemi goyon bayan mata a yaki da cutar polio

Dandalin gwamnonin Najeriya ya yi kira ga kungiyoyin mata da kananan hukumomi su bada goyon baya a kamfen yaki da cutar shan inna

Dandalin gwamnonin Najeriya ya yi kira ga kungiyoyin mata da kananan hukumomi su bada goyon baya a kamfen yaki da cutar shan inna a kasar.

Shugaban dandalin, gwamnan jihar Rivers Rt. Hon. Chibuike Rotimi Amaechi ne ya yi wannan kiran a Karamar hukumar Ikwerre ta jihar, yayinda yake kaddamar da rukuni na biyu na rigakafin cutar shan inna ta kasa da ake gudanarwa kwata kwata, wani shirin da dandalin gwamnonin yake aiwatarwa tare da hadin guiwar gidauniyar Bill da Milinda Gates.

Amaechi ya shawarci mata su rage zuwa neman maganin gargajiya a domin neman warkar da cutar shan inna, a maimakon haka ya bukace su, da su rika neman taimakon kwararrun likitoci.

Gwamnan wanda ya yiwa wadansu yara all’urar rigakafi yayin kaddamar da shirin, ya kuma yi kira ga al’ummar yankin su rika amfani da dakunan shan magani da gwamnatinshi ta gina domin kula da lafiyarsu.

Tun farko a cikin jawabin da yayi ga al’ummar jihar Rivers, gwamna Amaechi ya bayyana cewa kamfen din da aka ba lakabi da turanci “Women Against Polio” (WAP)-Mata masu yaki da shan inna- shine rukuni na biyu daga cikin hudu da za a aiwatar da nufin wayar da kan al’ummar Najeriya dangane da illar cutar da nufin kawar da ita a kasar baki daya.

Rukunin farko ya maida hankali a kan maza da ake kira “Men Against Polio” (MAP)-Maza masu yaki da cutar shan inna- Ganin ci gaban da aka samu na goyon bayan maza a yaki da cutar, aka kaddamar da rukuni na biyu wanda ya maida hankali kan neman goyon bayan mata. Kasancewa, mata sune suka fi kusa da kananan yara, banda haka kuma, sun iya tada tsimin al’umma.

Gwamnan ya kuma yi kira ga shugabannin kanannan hukumomi su bada hadin kai. Yayinda ya yiwa al’ummar jihar alkawarin samar da ingantaccen tsarin kiwon lafiya domin raba jihar da cutar shan inna.

Ra’ayinka

Show comments

XS
SM
MD
LG