Accessibility links

An kaddamar da wani shirin kula da mata masu juna biyu ta wayar salula


Wata mata da dan jaririn ta

An bayyana shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu don shawo kan mace macen mata bisa dalilai da suka shafi haihuwa.

An bayyana shirin kula da lafiyar mata masu juna biyu ta wayar salula a matsayin daya daga cikin muhimman hanyoyin shawo kan mace macen mata bisa dalilai da suka shafi haihuwa.

Shirin da ake kira “Mu ceci iyayenmu” ko kuma “Let’s Save Our Mothers” da turanci, wani shiri ne da wata kungiya mai zaman kanta “Traffinna Foundation” ta kafa da nufin fadakar da mata a kan al’adu da suke da illa ga lafiyarsu.

Cibiyar iganta rayuwar mata da kasa da kasa, Women Deliver, ta bayyana wannan shirin a matsayin daya daga cikin shirye-shirye hamsin da suke da taimako ainun a yunkurin shawo kan matsalar mace macen mata da kananan yara.

Shugabar shirin “Mu ceci iyayenmu” Chinomanso Traffina Ibe, wata ma’aikaciyar jinya a Najeriya, ta bayyana cewa, ta kirkiro da shirin ne da nufin ba mata dake zaune a yankunan karkara damar bayyana matsaloli da kalubalar da suke fuskanta dangane da kula da lafiyarsu da ta shafi ciki da haihuwa.

Cibiyar UNFPA ta bayyana cewa, wannan shirin zai taimaka wajen ceto rayukan mata a kasar da kimanin mace daya cikin 23 ke mutuwa sakamakon matsalolin haihuwa.

A cikin jawabinta, Jill Sheffield, shugabar cibiyar Women Deliver ta bayyana cewa, dabarun ceto rayukan mata da aka zayyana a shirye shirye hamsin da suka yi fice ya nuna cewa, za a iya inganta rayuwar ‘yan mata da kuma mata a kasashen duniya baki daya.

Daga cikin shirye shiryen shawo kan mace macen mata bisa dalilan haihuwa, guda hamsin da suka sami lambar yabo, 25 daga nahiyar Afrika yankin Hamada ne, tara daga yankin Asiya biyar daga Gabas ta tsakiya sai kuma hudu daga Latin Amurka biyu kuma daga kashen Turai da arewacin Amurka kowanne.

XS
SM
MD
LG