Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantaka Tayi Tsami Tsakanin Jamiyyun Kawance


‘Yan takarar shugaban kasa Rochas Okorocha, Sam Nida-Isaiah, Rabiu Kwankwaso, Muhammadu Buhari da Atiku Abubakar suna zaune a lokacin da suke gabatar da kudurinsu a babban taron APC, Disamba 11, 2014.

Ga bisa dukkan alamu dangantaka ta fara tsami tsakanin jamiyyun hadaka dake jihar Bauci, inda yayan jamiyyar CPC ke cewa ana nuna musu wariya bayan da aka kafa gwamnati.

Sabo da wannan dalilin ne yayan jamiyyar ke cewa zasu cire tutar jamiyyar APC a ofishin su.

Hajiya Hajara Ayuba it ace shugaban mata na jamiyyar CPC kuma ga abinda take cewa.

‘’Wallahi tallahi babu wani abu da aka yi, babu Magana mai dadi babu wani abu da aka yi, sai wata shiririta ta banza da wofi, wallahi ba buba wani abu da akayi, sai ma abin da ya karu na rashin mutunci ba, mu kuma ba zamu fasa fad aba, wallahi zaben kananan hukumomi na shugaban jamiyya, shugaban jamiyyar ta CPC yayi ruwa yayi tsaki yasa ciyamomin mu su suka zo suka tsaya aka zabi shugaban jamiyyar ta APC amma yanzu wai adawa ake yi da mutanen namu da suka tsaya aka zabi ciyaman din na APC, Yanzu abinda ake yi ba ayi dasu yadda kasan bayi haka suke a cikin garin Itas’’

Sai dai da aka tambaye ta to Kenan zasu cire tutocin APC Kenan a ofishisoshin nasu, sai ta amsa da cewa.

‘’Sai su cire tunda shugaban jamiyyar ta APC ba yayi dasu, ba wani abinda ake yi dasu sai dai su gani ana yi, ba zai yiyu ba, haka jamiyya ta mayar dasu kamar wadansu bayi.

Tace su mutanen jamiyyar CPC an ware su, tace yanzu kuma abinda ya rage shine sai kori Shugaba Buhari domi shima ai dan CPC.

Ga Abdulwahab Mohammed da Karin bayani ''4 13''

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

Bidiyo

Shugaban Gwamnatin Rikon Kwarya A Mali Goita Ya Tsallake Rijiya Da Baya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:34 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Sanarwar Neman Afuwa daga Malam Abdujabbar Kabara
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:36 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Shugaba Muhammadu Buhari Ya Yi Tattaki Gida Bayan Ya Idar Da Sallar Eid El-Kabir a Daura
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:06 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Zauren VOA: Najeriya da Kaubalen 'Yan Aware - 005
please wait

No media source currently available

0:00 0:22:55 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Matsalar Tsangwamar Mata Masu Saka Abaya A Kanon Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG