Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangantaka Tsakanin Flynn da Trump Ta Samu Rauni


Shugaba Trump da Janar Flynn tsohon mai bashi shawara kan harkokin tsaro
Shugaba Trump da Janar Flynn tsohon mai bashi shawara kan harkokin tsaro

Fadar White ta shugaban Amurka ta ce tun makonni uku da suka wuce aka shawarwaci shugaba Trump cewa, mai bashi shawara kan harkokin tsaro Michal Flynn, bai gayawa mataimakin shugban Amurka gaskiya ba kan maganar da yayi da jakadan Rasha a Amurka.

Kakakin fadar White House Sean Spicer, yace, tun lokacin Mr. Trump da hadimansa na kud da kud suke ta nazari da auna batun" "ko wace rana ko 'yan makonni za'a sallameshi kamin a ranar Litinin Flynn yayi murabus".

Gabannin shugaba Trump yayi rantsuwar kama aiki ranar 20 ga watan jiya, mataimakinsa Mike Pence ya fito a tashar talabijin ta CBS, a cikin shirinta na "Face the Nation" yace Flynn da jakadan Rasha a Amurka, basu yi magana kan takunkumin da Amurka ta kakabawa Rashar ba saboda rawarda ta taka a Ukraine.Haka nan mataimakin shugaban na Amurka Pence, ya kara da cewa jami'an biyu basu yi magana kan sabon takunkumin da gwamnatin Obama ta kakabawa Moscow cikin watan Disamba ba.

Da yake amsa tambayar 'yan jarida jiya Talata kan abunda ya sa ya dauki lokaci tsakanin 26 ga watan jiya zuwa ranar Litinin, kamin Flynn yayi murabus, Spicer, yace daga karshe shugaba Trump ya yanke shawarar cewa bashi da sauran wata yarda kan mai bashi shawara gameda harkokin tsaro ba.

A majalisar dokokin Amurka wakilai daga duka jam'iyun biyu, sun ce sun amince da murabus da Michael Flynn yayi a zaman mai baiwa shugaban kasa shwara kan harkokin tsaro.Daga nan suka shawarwci shugaba Trump ya kawo daidaito sabuwar gwamnatinsa a fuskar tsaro da ma sauran wasu sassa.

XS
SM
MD
LG