Accessibility links

Dangote Ya Ba Matan Jahar Kogi Naira Miliyan 220

  • Halima Djimrao

Alhaji Aliko Dangote

Aliko Dangote ya ce baiwa mata jari ne zai rage talauci

Aliko Dangote ya taimaki matan jahar Kogi da zunzurutun kudi har naira miliyan dari biyu da ishirin a matakin farkon tallafa mu su su fita daga kangin talauci. Mata dubu ishiri da biyu ne za su ci moriyar wannan tallafi a jahar ta Kogi. Aliko Dangote ya ce za a tallafawa mata a duka kananan hukumomin Najeriya guda dari bakwai da saba'in da hudu, amma ya ce sun fara da Kogi ne don gwamnatin jahar ce ta fara amince mu su, su yi hakan. Wakilin Sashen Hausa Ladan Ibrahim Ayawa ya tambayi Alhaji Aliko Dangote ko ina hikimar tallafawa mata kawai, sai ya kada baki ya ce:

XS
SM
MD
LG