Accessibility links

Jamhuriyar Nijar Zata Dauki Matakan Diflomasiyya


Shugaba Issoufou Mamane na Jamhuriyar Nijar

Domin tallafawa 'yan kasarta da hukumomi ke ta kamawa a Najeriya bisa dalilan da suka shafi harkokin tsaron yankin Arewacin Najeriya

Gwamnatin Jamhuriyar Nijar zata dauki wasu karin matakan diflomasiyya na kare martaba da mutuncin 'yan kasarta dake zaune a Najeriya, wadanda a cikin 'yan kwanakin nan suke fuskantar abinda suka kira tozartawa da cin mutunci daga jami'an tsaron Najeriya.

Ministan harkokin wajen Nijar, Bazzoum Mohammed, shi ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da 'yan kasar Nijar a ofishin jakadancin kasar dake Abuja, babban birnin Najeriya.

Bazzoum ya bayyana takaicin wasu hotuna da ya gani na yadda ake tsare 'yan Nijar, su na zaune ko tufa babu a jikinsu kamar wasu dabbobi. Yace wannan bai dace ba ko kadan, kuma ya saba da irin huldar 'yan'uwantaka dake tsakanin makwabtan biyu.

A cikin 'yan kwanakin nan dai, hukumomin kula da shige da ficen baki na Najeriya sun zafafa daukar matakan kamawa da tsarewa tare da tasa keyar 'yan Nijar da aka samu ba su da takardun zama a Najeriya. Wannan kuwa, yana da alaka ne da yadda harkokin tsaro suka tabarbare a yankin arewacin Najeriyar.

Wadannan matakan sun hasala 'yan Nijar din da dama, wadanda suka ce jami'an tsaron Najeriya su na tozartawa da kuma wulakanta su a irin wadannan lokutan.

Ga rahoton da Nasiru Adamu el-Hikaya ya aiko daga Abuja.

XS
SM
MD
LG