Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dangote Ya Kara Zabtare Farashin Dizel Dana Man Jirgin Sama Zuwa Naira N940 Da 980 Kowannensu


Kamfanin Mai Na Aliko Dangote
Kamfanin Mai Na Aliko Dangote

Shugaban sashen sadarwar na kamfanin, Mr. Anthony Chiejina, wanda ya sanar da cigaban a wata sanarwa, yace sabon farashin ya dace da kokarin da kamfanin ke yi na rage matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya.

WASHINGTON DC - Matatar man dangote ta sake zaftare farashin dizel da man jirgin sama zuwa Naira 940 da 980 akan litar kowannensu.

Hakan na zuwa ne bayan rage farashin zuwa Naira 1000 kan kowace lita da kamfanin yayi makonni 2 da suka gabata.

Sauyin farashin zuwa Naira 940 ya shafi kwastomomin kamfanin dake sayen lita miliyan 5 zuwa sama, a yayin da farashin 970 zai shafi kwastomomin dake sayen lita milyan guda zuwa sama.

Shugaban sashen sadarwar na kamfanin, Mr. Anthony Chiejina, wanda ya sanar da cigaban a wata sanarwa, yace sabon farashin ya dace da kokarin da kamfanin ke yi na rage matsin tattalin arzikin da ake fama da shi a Najeriya.

An ruwaito shi yana cewar, "matatar man Dangote ta kulla yarjejeniya da gidajen mai da iskar gas na MRS domin tabbatar da cewar abokan huldarmu sun sayi mai a farashi mai rahusa a gidajen man su dake biranen Legas ko Maiduguri. Kana iya sayen lita 1 ta dizel akan naira dubu daya da Naira 50 ko man jirgin sama akan Naira 980 a dukkanin tashoshin jiragen saman dake da gidan man MRS".

Ya kara da cewar zasu kulla makamanciyar wannan yarjejeniya da sauran manyan dillalan mai.

Manufar hakan itace, tabbatar da cewar masu sayen mai na yau da kullum basu saya da tsada ba, in ji shi.

Kasa da makonni 2 da suka gabata, hukumar gudanarwar matatar man Dangote ta sanar da sake zaftare farashin litar dizel daga Naira 1200 zuwa 1000.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG