Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Bakin Haure Suka Yi Zanga-zanga Jiya Alhamis A Birnin Washington


Bakin haure da suka yi zanga zanga jiya Alhamis
Bakin haure da suka yi zanga zanga jiya Alhamis

Daruruwan masu zanga-zanga ne suka yi dafifi jiya Alhamis anan birnin Washington, duk ko da irin sanyi da ake yi domin nuna abinda suka kira ranar da babu bakin haure a Amurka.

Wannan gangamin dai yasa da yawan shaguna da wasu wuraren kasuwanci sun kulle domin nuna goyon bayansu ga bakin hauren.

Wannan zanga-zangar dai ta biyo bayan umurni na musammam ne tare da aiwatar da wasu dokokin shige da fice da shugaba Trump ya bada umurnin ayi anfani dasu game da bakin haure, kuma umurnin ya hada da masu takardan shedan zama, mai kyau da kuma masu na bogi, ko kuma wanda suke tsaka tsaki. Duka wadannan rukunin ba wanda yasan makomar sa.

Cikin masu zanga-zangar na jiya Alhamis har da wani dan taliki mai suna Marcos, dan shekaru 34 mai aiki wurin sayar da abinci , yana dauke da katuwar tuta wadda ta isa nannade dansa dan shekaru 12suke tafiya tare wurin zanga-zangar wanda suka yi takawar kusan mil 3.

Zanga zangar bakin haure
Zanga zangar bakin haure

Sai dai ya hada tutar da kalar tutar kasarGuatemala dana Amurka inda yake zaune yau shekaru 12 kenan.

Shi dai wannan mai aikin dafa abincin ya yi kasadar da ‘yan uwan sa basu yi ba.

Kamar sauran manya-manyan gidajen sayar da abinci da suka kulle shagunan su a cikin Washington DC domin baiwa ma’aikatan su damar shiga cikin wannan zanga-zangar, saboda hakan ya nuna irin tasirin da bakin haure ke dashi a tattalin arzikin Amurka

Sai dai wasu ma’aikatan sun gaza zuwa domin anyi musu barazanar cewa muddin suka bi sahun wannan zanga-zangar to bakin aikin su abinda shiko Marcos yace ko an kore shi a wannan aikin zai iya samun wani.

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG