Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daruruwan Yara Sun Kamu Da Cutar Kyanda A Jihar Borno - Kungiyar Likitoci


Kungiyar likitocin kasa da kasa ta agaji ko kuma Doctors Without Borders / Médecins Sans Frontières (MSF) ta yi gargadin cewar, daruruwan yara na fama da cutar kyanda a Zabarmari, wani karamin gari a jihar Borno da ke fama da rikice-rikice.

Ana kuma bukatar yin allurar rigakafi don dakile cutar a Zabarmari da babban birnin jihar Maiduguri.

"Muna cikin tattaunawa da hukumomi kuma muna shirin tallafa musu a wani kamfen na riga-kafi da za a fara a Maiduguri da Zabarmari da zarar an samu allurar riga-kafin, saboda kyanda na da saurin yaduwa kuma tana da mummunar hadari musamman ga yara kanana," in ji David Thérond, MSF shugaban mishan din.

Har yanzu dai tattaunawar game da shirin riga-kafin na karkashin matakan jihohi da na tarayya tare da ma na Ma’aikatar Lafiya da Hukumar Lafiya ta Duniya.

MSF na kula da yara da suke fama da cutar kyanda a asibitin yara na Gwange da ke Maiduguri.

An kwantar da yaro na farko a ranar 3 ga watan Disamba, kuma adadin marasa lafiya ya karu tun daga lokacin a asibitin Gwange da ma sauran asibitocin Maiduguri.

Daga 1 ga Janairu zuwa 3 ga Afrilu, MSF ta kwantar da yara 1,158 da ke fama da cutar kyanda a asibitin yara na Gwange, wanda kashi 58 cikin ɗari suka fito daga Zabarmari, da ke da nisan mil 12 daga Maiduguri.

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG