Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daso Ta Bayyana Bangaren Da Yake Burge Ta A Fim Din “Labarina”


Nafisa (hagu) da Daso (dama) a lokacin da ake daukan shirin Labarina zango na 3 (Instagram/Daso)
Nafisa (hagu) da Daso (dama) a lokacin da ake daukan shirin Labarina zango na 3 (Instagram/Daso)

Jarumar ta kuma lakancin fannin fitowa a matsayin mai barkwanci wanda shi ma takan nishadantar da masoya fina-finan Kannywood da abubuwan ban dariya.

Fitacciyar jarumar Kannywood a Najeriya, Saratu Gidado, wacce aka fi sani da Saratu Daso, ta wallafa wani bangare na shirin “Labarina” mai dogon zango, inda ta bayyana shi a matsayin bangaren da yake sa ta “nishadi.”

Daso ita ce Innar Lukman (Yusuf Saseen) a shirin wanda yake so ya auri Sumayya (Nafisa Abdullahi.)

Jarumar ta wallafa bangaren da ta fito fili ta nuna rashin yardarta da Sumayya a matsayin wacce Lukman yake so ya aura.

“Kar ka bata wa kanka lokaci, ke kuma bari na gaya miki, Lukman bai isa ya yi aure ba idan ban aminta ba.” Daso ta fada a cikin shirin, wanda ta wallafa wani dan bangare na bidiyo.

“Bangaren da na fi so kenan yake kuma sa ni nishadi a cikin fim din Labarina.” Daso ta rubuta a shaifnta na Instagram hade da bidiyon.

Yusuf Saseen (Instagram/ Yusuf Saseen)
Yusuf Saseen (Instagram/ Yusuf Saseen)

Ga dukkan alamu, Daso ta ki amincewa da Nafisa ne saboda a iyi kiyasin da ta yi, Lukman ya fi karfinta duba da cewa ita ‘yar waka ce a fim din wanda kamfanin Saira Movies na Amin Saira ke shiryawa.

Ita dai Daso, ba bakuwa ba ce a fannin fitowa a matsayin mai fada da nuna ba-sani-ba-sabo a fina-finan Hausa, inda ta kan sa kwalli a ido ta baje abin da ke ranta.

Hakan kuma ya sa ta yi fice a fagen shirya finan-finan Hausa, har ma ta kai ga idan ba ta nuna irin wannan halayya ba, ba kasafai take burge masu kallo ba.

Jarumar ta kuma lakancin fannin fitowa a matsayin mai barkwanci wanda shi ma takan nishadantar da masoya fina-finan Kannywood da abubuwan ban dariya.

To ashe ita ma ga dukkan alamu, ta fi kaunar wannan matsayi na fitowa a mafadaciya.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG