Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dattawan Arewa Sun yi Watsi da Sakamakon Taron Kasa na Jonathan


Ibrahim: Mai ya sa ku kayi watsi da wannan rahoto mai mahimnci?

Ango:Domin wadanda suka rubuta rahoton ba wakilan Najeriya bane.

Ibrahim:A lokaci da ake yi taron mai yasa ba ku ce ba ku amince da taron ba?

Ango:Mun fada babu iyaka cewa wannan taro na Jonathan ne shi ya nada wakilan da suka je kuma idan taron kasa ne na wadanda ke neman duba tsarin mulkin kasa wanda muka saba yi kowane ciki sai an baiwa mutanen kasa dama zaban wakilan da zasu wakilce su, ni anyi dani sau uku 1987,1994 da 2005, duk ba wanda ba sai da aka yi zabe a mazabata ba kafi in zama wakili ba, saboda haka wana mutane da aka tara ba wakilan Najeriya bane na gaskiya wakilan Jonathan ne su je su rubuta abun da yake so shi kenan.

Ibrahim: amma daga cikin su a'i akwai dattawa daga arewacin Najeriya?

Ango: Toh dama cewa aka yi babu mutanen arewa, amma mu matsayin mu na kungiyar dattawan arewa ba mu yarda da taron ba, kasan a dattawan arewa akwai ‘yan ku ci ku bamu a ciki ko a’I kafi ni sani kai dan jarida ne.

Ibrahim: Ko zaka gaya mana takamaiman sassan da baku yarda da shi ba?

Ango: Taron ne gaba daya bamu yarda da shi ba domin ba’a tsara shi ba irin yadda zai zama taron kasa ba, gaba dayan shi ne muka ce dalilin da yasa muka yi watsi da duk a’i ba za’a ce kila akwai wasu abubuwa da aka shswarta kamar na kirki ba, amma da yake taron bashi da tushe shi ya sa mu k ace duk ayi watsi da shi gaba daya.

Ibrahim: Toh ba ku ganin wasu zasu ce bangaranci ne kuka yi?

Ango: Kwarai da gaske a’i bangarancin aka yi, aka yi taron, taron ma bangaranci ne.

Ibrahim Kenan Farfesa,ba’a yi dai dai ba kuma sai ba kuyi dai dai ba?

Ango: Way a far ba dai dai bam un ce taron nan idan ma za’a yi shi ga yadda za’a yi shi aka ki ji ko kwamitin da ya nada suka kewaya su ji ra’ayin mutane rahoton sun a farko ya nuna cewar mutanen kasa sun ce idan za’a yi taro a tabbatar da taron ne na zababboun mutane kuma mutanen sassan kasar nan zasu zabo su a’i ba’a yi haka ba saboda haka.

Ibrahim: To Farfesa ina ma fita dagane da abubuwan da aka zaiyana a matsayin suke kawo matsala a Najeriya?

Ango: Wannan kuma za’a samu wani lokaci wanda mutanen Najeriya zasu yarda da tsarin da zai zama za’a tura wakilan sun a gaskiya su je su duba al’amuran da suka damu Najeriya wannan shine kadai mafita.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:03:10 0:00

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG