Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Davido Ya Taya Burna Boy, Wizkid Murnar Lashe Lambobin Yabo Na Grammy


Davido, (hagu) Burna Boy (tsakiya) Wizkid (dama) (Hoto: Shafukansu na Instagram)
Davido, (hagu) Burna Boy (tsakiya) Wizkid (dama) (Hoto: Shafukansu na Instagram)

“Ko ta wacce fuska ka kalli wannan (lambar yabo,) babbar nasara ce ga Najeriya, al’adunta, da al’umarta! Ina taya dukkan wadanda suka samu wannan kyauta murna!" In Ji Davido.

A wani lamari da ya ba mutane da dama mamaki, fitaccen mawakin Afrobeat a Najeriya David Adeleke wanda aka fi sani da Davido, ya taya takwarorin sana’arsa Burna Boy da Wizkid murnar lashe lambar yabo ta Grammy da aka yi Amurka.

An karrama Burna Boy ne a matsayin mawakin da kundin wakokinsa ya fi fice a duniya yayin da shi kuma Wizkid ya lashe kyautar mawakin da hoton bidiyon wakarsa da ya yi da Beyonce (Brown Skin Girl) ya kasance wanda ya fi kayatarwa.

“Ko ta wacce fuska ka kalli wannan (lambar yabo,) babbar nasara ce ga Najeriya, al’adunta, da al’umarta! Ina taya dukkan wadanda suka samu wannan kyauta murna! #Grammys #foreverchoke” Davido ya rubuta a shafinsa na Twitter.

Kundin wakar na Burna Boy, wanda ya ba shi damar samun lambar yabon shi ne “Twice as Tall,” wanda ya sake shi a watan Agustan 2020.

Shi dai Davido wanda ya rera wakar “Jowo” a baya-bayan nan, bai taba lashe wannan kyauta ta Grammy ba, wacce aka yi bikin a birnin Los Angeles na Amurka a ranar 14 ga watan Maris.

Wannan shi ne karon farko dai da mawakan Najeriya suka samu wannan lambar yabo a bikin na Grammy wanda aka yi shi a juko na 63.

Gwamnatin Tarayya Ta Taya Burna Boy, Wizkid Murna

Ita ma gwamnatin tarayya a Najeriya, ta bi sahu wajen mika sakon taya murnarta ga mawakan.

Cikin wata sanarwa da Ministan yada labarai da al’adu Alhaji Lai Mohamed ya fitar, gwamnatin ta yaba da wannan karrama ‘yan kasarta da aka yi.

Alhaji Lai Mohammed
Alhaji Lai Mohammed

“Muna fatan wannan karramawa da aka yi wa mawakn biyu, bawai kawai za ta zaburar da su domin kai wa ga wani mataki na kololuwa ba ne, muna fatan za zama zamanto abin kwadaitarwa ga sauran jama’a.” Mohammed ya ce cikin sanarwa wacce aka wallafa a shafin Twitter na mataimakinsa Olusegun Adeyemi

‘Yan Najeriya Sun Barke Da Murna, Muhawara a Shafukan Sada Zumunta

Tun a yammacin jiya, masoya wakokin Afrobeat suka mamaye shafukan sada zumunta, musamman a Najeriya, don nuna murnarsu da kuma tafka muhawara kan wadannan kyaututtuka.

A gefe guda, masoya Burna Boy wanda ake yi wa lakabi da “African Giant,” suke ta nuna cewa gwarzon na su ya nunawa duniya cewa shi ne sarki a fagen wakokin Afrobeat kamar yadda su ma na Wizkid suke nunawa.

A wani gefen kuma masu adawa da su, mafi aksari masoyan Davido na nuna cewa ba su cancanci wadannan lambobin yabo ba.

Rikici Na Baya-bayan Nan Da Ya Faru

Taya murnar da Davido ya yi ta shammaci mutane da dama, lura da cewa ba a ga maciji tsakaninsa da wadannan mawaka, musamman da Burna Boy, wanda har dambe suka yi da shi a wani gidan rawa a Ghana a watan Disambar bara.

A lokacin fadan, Wizkid na zaune a gidan rawar, kuma bai yi yunkurin ya shiga tsakanin Davido da Burna Boy ba, kamar yadda hotunan bidiyon da aka yi ta yadawa a shafukan sada zumunta suka nuna.

Burna Boy
Burna Boy

A ko da yaushe, mawakan kan shiga shafukan sada zumunta suna jefawa junansu bakaken maganganu cikin kalamai na haibaici. Ko wane mawaki cikinsu kan yi ikrarin shi ya fi iya wakar Afrobeat.

Tarihi ya nuna cewa mawakan na dasawa a baya, amma sun fara samun sabani ne yayin da kowannensu ke ganin shi aka fi so.

Kuma dukkansu suna da masoya a sassan duniya musamman a Amurka da ake mata kallon dandalin mawakan duniya.

Yawan Masoya a Shafukan Sada Zumunta

Wani ma’auni da wasu ke amfani da shi wajen nuna karbuwar dan waka ga jama’a shi ne adadin wadanda ke bin mawaki a shafukan sada zumunta, ko da yake wasu na nuna cewa wannan ba shi ne ma’aunin da ya kamata a yi amfani da shi ba.

Wizkid (Hoto: Shafin Instagram)
Wizkid (Hoto: Shafin Instagram)

Davido na da masoya miliyan 19.3 a Instagram, Burna Boy na da miliyan 6.2, Wizkid na da miliyan 11.8.

A shafin Twitter kuwa, Davido na da masoya miliyan tara, Burna Boy na da miliyan biyar yayin da Wizkid wanda ya yi wakar “Joro” yake da miliyan 8.3.

Bidiyo

Saurari Dalilin Da Ya Sa Ummi Zeezee Ta Ce Tana So Ta Kashe Kanta A Hira Da Wakiliyar VOA Baraka Bashir
please wait

No media source currently available

0:00 0:06:39 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Saurari Bayanin Jarumar Kannywood, Nafeesa Abdullahi
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:24 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

VOA CASU

VOA CASU: Bikin Yini Na Auren Zawarawa A Kano
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG