Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

De Mistura na Shirin Kafa Kwamitin Tsara Kudin Tsarin Mulkin Syria


Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman a Syria, Staffan De Mistura
Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na Musamman a Syria, Staffan De Mistura

Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman a Syria, Steffan de Mistura yace masu tattaunawa samun zaman lafiya a birnin Sochi na kasar Rasha, sun amince da kafa wani kwamitin da zai shirya daftarin sabon kundin tsarin mulkin kasar.

Staffan de Mistura ya fadawa manema labarai a New York ta wayar tarho da daren jiya Talata daga Otal, cewa wadanda suka shirya zaman tattaunawar da suka hada da Rasha da Iran da kuma Turkiya kowanensu sun bashi shawarar sunayen mutanen hamsin, wakilan kwamitin da za’a kafa. Yace za su hada da wakilai daga gwamnatin Syria da na yan adawa da ma masu zaman kansu.

De Mistura yace ya himmantu wurin tabbatar da kwamitin kundin tsain mulkin. Sai dai kwararen jami’in na diplomaisya bai bada bayani akan lokacin da kayyade na sanar da tsarin da yayi ko ranar da kwamitin zai fara zaman shirya kundin tsarin mulkin.

Ya kuma tabbatar da cewa aiki dake gabanmu yana da sarkakiya. Amma kuma yace su imanin za’a iya samun ci gaba daga nan.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG