Masu kada kuri’a a zaben sharar fage na fidda da gwanin da zai kara da shugaba Donald Trump a zaben watan Nuwamba sun fara jefa kuri'unsu.
Zaben na zuwa ne yayin da kowanne dan takarar da ke neman tikitin jam’iyyar ke kara kaimi wajen ganin an zabe shi.
Jim kadan bayan 12 dare masu kada kuri’a suka yi zabe a Dixville Notch a jihar ta New Hampshire, inda tsohon Magajin Garin New York Michael Bloomberg ya samu kuri’u biyu, sannan Sanata Bernie Sanders da Pete Buttigieg suka samu kuri’u daya-daya.
Mafi aksarin rumfunan zaben za su bude ne da safiyar yau, inda kuma ake sa ran fitar da sakamakon zabe a yammacin yau Talata.
Sai dai Shugaba Donald Trump, ya mayar da martani kan zaben na ‘yan Democrat
“Damuwata ita ce, ina kokarin fahimtar wane ne dan takara mafi rauni a cikinsu, kai! ina ga dukkansu ma masu rauni ne".
Facebook Forum