Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DFID Na Tallafa wa Bangaren Shari'ar Kano


Alamar doka da kuma zartaswa

Hukumar Raya Kasashe ta Burtaniya, DFID a takaice, za ta cigaba da taimaka wa bangaren shari'ar jihar Kano

Hukumar Raya Kasashe Ta Kasar Burtaniya, Department for International Development (DFID) a Turance, ta dukufa wajen agaza wa bangaren Shari’a na Jihar Kano a karkashin wani shiri mai suna Wanzar Da Adalci Ga Kowa (Justice For All Program a Turance. )

Jami’ar shirin na Justice For All a Arewa maso yammacon Nijeriya Hajiya A’isha Abubakar ta ce irin taimakon da su ke bayarwa ga bangaren na shari’a sun hada har da ankarar da bangaren na shari’a idan ya kauce hanya; akwai kuma tallafin kudade da kayan aiki da sauransu.

Malama A’isha ta gaya ma wakilinmu a Kano Mahmud Ibrahim Kwari cewa wani sa’in kuma hukumar kan hada hannu da bangaren na shari’a wajen shirya wasu abubuwan amfanar da jama’a game tsarin doka da dai sauransu.
Wakilin na mu ya kuma ruwauto wani dan Majalisar Dokokin jihar Kano mai suna Hon Gambo Sallau na cewa Majalisar ita ma za ta kwaskawre bangaren na shari’a saboda adalci ya kankama a jihar.

Shi ma Attoni-Janar kuma Kwamishinan Shari’ar jihar Kano, Barrister Maliki Kuliya Umar, y ace Ma’aikatar Shari’ar Kano za ta taka muhimmiyar rawa wajen ganin an cimma wadannan gurorin.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:18 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG