Accessibility links

Tsohon gwamnan jihar Kano ya ce ba zasu bari 'yan tawayen PDP su shiga jam'iyyarsu ta APC ba sai an tantancesu.

Tsohon gwamnan jihar Kano Malam Ibrahim Shekarau ya ce koda gwamnonin nan bakwai na PDP dake rigima da jam'iyyarsu sun nemi su shiga jam'iyyar APC dole sai an shimfida masu wasu ka'idodi domin kada su kawo akidarsu ta PDP.

Yayin da yake jawabi a taron da wasu kungiyoyi biyu suka shirya kan neman hanyar warware matsalolin da suka addabi Najeriya Malama Ibrahim Shekaru ya ce su gwamnonin dake takardama da jam'iyyarsu ba wani gaskiye ne suke da shi ba. Ya ce idan har suka nemi su shigo jam'iyyar APC ba za'a yarda su shigo da halin zalunci ba ko halin satar kuri'a da danniya da suka saba yi a jam'iyyar PDP. Ya ce ba zasu yadda da shakiyan da ke cikin jam'iyyar PDP ba.

Dangane da baraka dake tsakaninsa da Janaral Buhari a da can kafin su narke cikin jam'iyya daya Malam Ibrahim ya ce basu taba samun baraka ba sai dai suna cikin jam'iyyu daban daban ne. Yanzu da suke jam'iyya daya ya ce ya yarda idan Janaral Buhari zai nemi tsayawa takarar shugabn kasa to shi zi yanye masa. Shi kuma Malam El-Rufai ya ce kodayake can farko wani bangaren jam'iyyar APGA ya yi kyamar shiga APC amma yanzu wasu jiga-jigan jam'iyyar sun soma shiga APC. El-Rufai ya ce APGA reshen gwamna Obi dama can PDP ce amma sun hakura da shi. Bayan hakan ciyamomi 22 na APGA cikin 36 sun shiga APC don haka basa son wasu shakiyai shaidanu su shigo jam'iyyarsu wadanda ba zasu taba tuba ba.

Daya daga cikin shugabannin da suka shirya taron Hajiya Hafsat Mohammed Baba ta yi bayanin dalilin shirya taron. Ta ce sun shirya shi ne domin hada kan mutanen Kaduna da wayar masu da kawunansu domin a yi tafiya tare. Wani makasudin taron kuma jama'a su sadu da wasu daga cikin jam'iyyar APC, su tattauna da su yadda za'a samu mafita daga irin halin da kasar ta samu kanta a ciki.

Isah Lawal Ikara nada rahoto.

XS
SM
MD
LG