Hakan na nufin Costa zai koma garinsa na Sao Paulo bayan da ya kwashe shekara 15 yana wasa a nahiyar turai.
Dan shekara 32, Costa wanda ya bar Atletico Madrid a watan Janairu, yana kan tattaunawa da kungiyar ta Palmeiras wacce tana daya daga cikin gaggan kungiyoyin wasan kwallon kafa a Sao Paulo.
Kungiyar ta yi masa tayin kwantiragin shekara biyu kan kudi pam miliyan 2.6 bayan an cire haraji. Rahotanni sun ce yanzu haka dan wasan har ya isa kasar ta Brazil a cewar shafin yanar gizo na Sky Sports.
Baya ga kungiyar ta Palmeiras, akwai kungiyoyin da suke tattauanawa da Costa a Turkiyya, Qatar da Saudiyya tun bayan da ya fice daga Madrid.
Rahotanni sun ce kungiyar Al-Shabab ta Saudiyya ta kusanci kulla yarjejeniya da shi amma ba a samu jituwa ba a karshe.
Hakazalika akwai kungiyoyi a gasar Premier League da suka nuna sha’awar sayensa amma abin ya cutura.