Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Direbobi Na Zanga-Zanga Kan Karbar Na Goro Da Jami’an Tsaro Ke Yi


Direbobi sun tare hanya don nuna fushi ga jami'an tsaro.

Direbobi sun rufe babbar hanyar da ta hada Adamawa da jihar Taraba sakamakon matsa musu da karbar na goro da jami'an tsaro ke yi.

Wasu direbobi sun datse babbar hanyar da ta hada jihar Adamawa da Taraba, a Mayo Belwa, domin nuna fushinsu bisa zargin da suke yiwa jami'an tsaro na taresu da karbar na goro, musamman ranakun da kasuwanni ke ci.

Haka kuma matafiya da kuma yan kasuwa na kokawa game da wannan lamari.

An kwashe tsawon lokaci kafin shawo kan lamarin, yayin da rundunar yan sandan jihar Adamawa ta ce za ta dau mataki.

SP Othman Abubakar dake zama kakakin rundunar yan Sandan jihar Adamawa, ya bayyana cewa za a ladabtar da duk wani jami’in da aka samu da irin wannan laifin.

Domin karin bayani saurari rahotan Ibrahim Abdul’aziz.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:36 0:00

Facebook Forum

Matsalar Tsaro A Zamfara

Ko Kun San Irin Makaman Da Sojoji Ke Amfani Da Su Wajen Yaki Da 'Yan Bindiga A Jihar Zamfara?
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:31 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Kamu A Auren Nupawa

Yadda Nupawa Suke Kamun Ango A Bikin Aure
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG