Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Majalisar Dattawa Ta Yi Watsi Da Bukatar Yi wa Jadawalin Zabe Garambawul


Majalisar Dattawan Najeriya
Majalisar Dattawan Najeriya

Cece-ku-cen da 'yan majalisun tarayyar Najeriya suka dinga yi akan yi wa jadawalin zabe gyaran fuska ya kawo karshe saboda majalisun biyu, na wakilai da na dattawa sun yi watsi da yunkurin, ke nan za su yi aiki da yadda hukumar zabe ta tsara za ta gudanar da zaben badi.

Majalisar Dattawan Najeriya ta yi watsi da yunkurin yi wa jadawalin zaben shekara mai zuwa garambawul.

Hakan ya faru ne saboda yunkurin bai samu isasshen goyon baya ba da gyaran ya fuskanta a majalisun wakilai da na dattawa lokacin da aka gabatar da shi a zamansu.

Mambobin sauran jam'iyyun sun yi tir da yunkurin musamman ma a majalisar dattawa jim kadan bayan da shugaban kwamitin zabe na majalisar Suleiman Nazir ya yi kokarin farfado da maganar.

Duk da umurnin da mataimakin shugaban majalisar dattawan ya bai wa kwamitin cewa yana iya sake waiwayar maganar, Sanata Kabiru Gaya nan take ya hango abun da ya kira sakin layi.

Ya ce babu amfanin yi wa jadawalin garambawul a daidai lokacin da suke kokarin rage kashe kudi akan zabuka.

Kamata ya yi a samu yadda za'a tallafawa talakawa ba a kasa zabe gida uku ba. Yadda hukumar zabe ta shirya a yi shi ya fi alheri, injishi.

Ga rahoton Medina Dauda da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG