Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Direbobi Sun Hallaka Dan Sanda Yayin Karbar Na Goro


Rahotanni daga jihar Adamawa arewa maso gabashin Najeriya na cewa wasu direbobi sun harzuka har sun kashe wani dan sanda kan karbar na goro.

Kamar yadda rahotanni ke cewa dan sadan ne ya soma bude wuta ga wasu direbobi dake kan hanyar zuwa cin kasuwa bayan ya nemi su bashi cin hanci, koda suka bashi Naira hamsin sai ya ki karba.

A kan haka ne ganin suna kokarin kama hanyar tafiya sai kawai ya budewa direbobin wuta, lamarin da ya har zuka fasinjoji suka yi masa a ture.

Rundunar 'yan sandan jihar Adamawa ta tabbatar da aukuwar lamarin inda ma kakakin rundunar SP Othman Abubakar, ya ce suna bincike.

Yanzu haka dai akwai alamun sauran rina a kaba game da umarnin cire shingayen binciken 'yan sanda da kuma karbar cin hanci da sufeta janar na 'yan sandan Najeriya, Ibrahim Idris, ya bada a makon jiya.

Wannan umarni dai da farko yasa 'yan Najeriya, da yawa yin maraba da wannan mataki domin galibi shingayen tamkar hanyar damar karbar na goro ce daga matafiya da kuma masu jigilar kayayyaki.

Domin karin bayani saurari rahoton Ibrahim Abdul'aziz a nan.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG