Accessibility links

Dogarawa Mata Zasu Kare Hakkin Mata A Jihar Ogun


Wannan hoto na mata ne masu hallartar taro akan lafiya.

Gwamnan jihar Ogun, Ibikunle Amosun ya kaddamar da dogarawansa mata zalla da aka kira Metro, wadanda zasu yi aikin kare ‘yancin mata, da ilimantar da su a game da sanin ‘yancin su, da kuma hana mata shiga bangar siyasa a kakar zabubbukan shekara ta 2015 idan Allah Ya kaimu.

A jiya juma’a ne, Gwamna Amosun ya kaddamar da rundunar matan a filin wasan MKO Abiola dake unguwar Kuto, a cikin birnin Abekuta fadar jihar Ogun.

Gwamnan yace ya ji dadin abinda ya shaida ya kuma gani, a game da dogarawan Metro. Gwamnan ya bukace su da su kasance masu gaskiya kana su kaucewa kin gudanar da ayyukansu na sa kai. Yace zai yi kokarin tallafa musu domin su ji karfin gudanar da ayyukansu.

Mai dakinshi, uwargida Olufunsho Amosun tace Metro, dogarawan sa kai ne kuma ba’a biyansu albashi, kuma suna nuna halaye na gari. Mrs. Amosun ta kuma yi kira da jama’a da su baiwa dogarawan hadin kai da goyon baya domin su yi nasara a ayyukansu.

Dagorawan wadanda dukkaninsu mata ne sun bazu a kananan hukomi 20 a duk fadin jihar.

XS
SM
MD
LG