Alhazan jahohin Adamawa da Taraba sun gama shiri, saura tashi.
WASHINGTON, DC —
A daidai lokacin da ake kaddamar da jigilar Alhazan Najeriya a yau asabar, hukumomin farali, a yayin da hukumomin jahar Adamawa su ka zakulo wasu mata masu ciki da suka yi kokarin yin layar zana su je kasar Saudiyya duk kuwa da fadakarwar da aka yi ta yi game da kasadar da ke tattare da zuwa aikin Hajji da ciki. Tuni dai an dakatar da wadannan mata kuma an dauki mataki a kan su kamar yadda babban sakataren hukumar alhazan jahar Adamawa Alhaji Saluhu Danjumma Usuman ya tabbatarwa wakilin Sashen Hausa Ibrahim Abdulaziz. Haka kuma Alhaji Saluhu Danjumma Usuman ya ce a bana jahar Adamawa ta dauki sabbin matakan takaita galabaita a sansanonin alhazai.
Za ku iya son wannan ma
-
Fabrairu 09, 2023
Zaben 2023: Siyasar Jihar Kaduna
-
Fabrairu 09, 2023
Kamfanin Man NNPC Zai Fara Saida Wa Dillalan Man IPMAN Mai Kai Tsaye
-
Fabrairu 08, 2023
Ana Fafutuka Da Tafka Dambarwa A Gaban Bankunan Najeriya
-
Fabrairu 08, 2023
Kotun Koli Ta Dakatar Da Wa’adin Daina Karbar Tsoffin Kudi