Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Hana Sayar Da Kayan Shaye Shaye Masu Zaki a New York?


Magajin Garin New York Michael Bloomberg.

Magajin garin New York Michael Bloomberg yana shawarar hana sayar da kayan shaye shaye masu zaki da irinsu, a kokarin yaki da kiba da ke kara karuwa a birnin na New York.

Magajin garin New York Michael Bloomberg yana shawarar hana sayar da kayan shaye shaye masu zaki da irinsu, a kokarin yaki da kiba da ke kara karuwa a birnin na New York.

A ranar laraba Mr.Bloomberg ya bada sanarwar haka, wadda itace irin ta ta farko a duk fadin Amurka. Dokar idan ta tabbata zata haramtawa wuraren cin abinci, da na shakatawa da gidajen sinima, da dandalin wasanni sayar da kayan shaye shaye a manyan kolabe da suka haura nauyin milimita 450 da hamsin.

Amma hanin ba zai shafi kayan shaye shaye da aka yi da nufin rage kiba, kamar su Diet Coke, da ruwan ‘ya’yan itatuwa, da kuma giya.

Kudurin ba zai zama doka ba sai hukumar kiwon lafiya ta New York wadanda wakilanta duka magajin garin na yanzu ne ya nada su, sun amince da shi.

Wani kakakin kungiyar masu hajar kayan shaye shaye masu zaki a New York ya soki shawarar Mr. Bloomberg da cewa zumudi ne da neman wuce makadi da rawa, daga nan yayi kira ga jami’an kiwon lafiya su nemi hanyoyin magance yawan kiba da masu amfani.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG