Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Ta Baci: Kungiyoyi Da Mazauna Jihohin Borno Da Yobe Da Adamawa Na Kokawa


An daina ganin wayar selula a hannun jama'a haka a Borno, Yobe da Adamawa saboda ba su aiki
An daina ganin wayar selula a hannun jama'a haka a Borno, Yobe da Adamawa saboda ba su aiki

Mazauna jihohin Borno da Yobe da Adamawa da kuma kungiyoyi masu zaman kan su na cigaba da kokawa kan rashin sadarwa ta wayar selula da kuma zargin gallazawa.

A yayin da sojojin Nijeriya ke cewa su na cigaba da fatattaka da kuma farautar 'yan kungiyar Jama'atu Ahlis Sunna Lid Daawati Wal Jihad, da ake wa lakabi da Boko Haram, su kuma mazauna jihohin da aka kakaba wa dokar ta bacin sun ce al'amarin na wajiga su; ga kuma rashin sadarwa ta wayar selula.

Wakilinmu na jihar Adamawa, Ibrahim Abdul'aziz, ya tattauna da wasu mazauna wadannan jihohin da su ka ce sanadiyyar kafa dokar ta bacin su na fama da talauci da rashin farinciki. Ga shi kuma babu damar su kira 'yan uwansu su dauke kewa su kuma yi zumunci.

Haka zalika, wasu 'yan Kungiyar Dattawan Arewa, Malam Abdulrazaq Yola da Barrister Solomon Dalong, sun yi Allah wadai da katse layukan sadarwan. Su ka ce ba haka ake yi ba a sauran wuraren da ake tashin hankali. Sun kuma yi zargin cewa ana gallaza wa jama'a ne kawai saboda tuni 'yan Boko Haram su ka ketara zuwa makwabtan kasashe da su ka ji za a far masu.

Korafi Kan Rashin Wayar Selula a Borno, Yobe Da Adamawa - 2:00
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:04 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG