Accessibility links

Sojoji Sun Ce Sun Wargaza Gagarumin Harin Ta'addanci A Maiduguri

  • Garba Suleiman

Sojoji su na sintiri a Jihar Borno

Rundunar sojan Najeriya ta kuma ce ta kama daya daga cikin mutanen da aka fi nema ruwa a jallo a kasar mai suna "Abba" a wani fadan da aka gwabza

Rundunar sojojin Najeriya ta ce ta kashe ‘yan tawaye 3, ta kama wasu guda 25, a lokacin da take tarwatsa wani mummunan harin ta’addancin da aka shirya kaiwa a garin Maiduguri a yankin arewa maso gabashin kasar.

A bayan wargaza w3annan harin da aka yi niyya tare da kashewa ko kama wadanda suka shirya kai shi, rundunar sojojin ta Najeriya ta ce ta tare wasu sakonnin dake yin kira ga ‘ya’yan kungiyar Boko Haram da su tsaya su yaki abinda rundunar sojan ta kira gagarumin farmakin da aka kaddamar a kan kungiyar.

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta kuma ce ta kama daya daga cikin abinda ta kira ‘yan ta’addar “da aka fi nema ruwa a jallo” a fadin Najeriya, mutumin da aka ce sunansa Abba kawai, yayin da aka kashe sojan gwamnati guda daya a wannan fada.

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta ce wuraren gudu sun yi kadan ma ‘ya’yan kungiyar dake arcewa a saboda a yanzu garuruwan bakin iyaka da dama su na hannun sojojin gwamnati.

Sai dai babu hanyar sadarwa ta jama’a, an toshe hanyoyin mota, kuma babu ‘yan kallo masu zaman kansu a bakin daga, don haka babu wata hanya mai zaman kanta ta ta bbatar da sahihancin rahotannin da sojojin suke bayarwa.

Wasu masu fashin baki su na bayyana fargabar cewa tsinke hanyoyin sadarwar wata dabara ce da gwamnati ta bullo da ita domin rufe idanun duniya daga ayyukan keta hakkin bil Adama da sojojinta ke yi. Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na kasashen duniya da kuma gwamnatin Amurka sun zargi sojojin Najeriya da laifin kashe mutanen da suke zargi maimakon su kama su, ko kuma kama mutum ba tare da wata shaida ba.
XS
SM
MD
LG