Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokar Zabe: Yadda Kungiyoyin Fararen Hula Suka Yi Zanga-Zanga A Abuja


Lokacin zanga-zangar Endsars (Mun yi amfani da wannan hoto don nuna misalin zanga-zanga)
Lokacin zanga-zangar Endsars (Mun yi amfani da wannan hoto don nuna misalin zanga-zanga)

A cewar kakakin Buhari, Femi Adesina, rashin sanin abin da kundin tsarin mulkin kasa ya kunsa ne ya sa wasu suke ta kurarin da suke yi saboda ba a saka hannu a kudurin dokar ta zabe ba.

Kungiyoyin fararen hula da masu sa ido kan lamuran zabe sun gudanar da gagarumar zanga-zanga a Abuja don matsa lamba ga shugaba Buhari ya sanya hannu kan sabuwar dokar zabe.

A yanzu haka dokar zaben da a ka sake gyarawa na gaban shugaba Buhari da a ke ganin lokacin na kurewa na yiwuwar amfani da dokar ko da an amince da ita.

Masu zanga-zangar sun ta’allaka nasarar adalcin zabe bisa amincewa da sabuwar dokar da a ke ta jeka-ka-dawo da ita tun gabanin zaben 2019.

Shugaba Buhari na jan kafa kan sabuwar dokar don abubuwan da bai gamsu da su ba musamman zaben ‘yar tinke a fidda ‘yan takara da ya ke cewa zai ci kudi ga kalubalen tsaro; inda hakan ya sa cire wannan babi da kuma sauya fasalin dokar da ya hada da mai son takara ya sauka tukun daga mukamin sa.

Paul James na kungiyar sanya ido kan zabe mai suna ‘YIAGA” da ke nuna ya kamata shugaban ya saurari bukatun jama’a.

Su ma mata ba a bar su a baya ba wajen zanga-zangar. Maryam Hamman da ke bangaren mata ta ce hatta inganta lamuran dalibai a makarantu na da nasaba da dokar zabe mai inganci.

Suleiman Adamu da ke wakiltar wata kungiyar matasan arewa ya ce sanya hannu kan dokar ka iya ba da dama ga amfani da na’ura wajen tura sakamako don kaucewa magudi.

Sai dai cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Litinin, Kakakin Buhari, Femi Adesina ya ce doka ta shugaban kasar damar tsawon kwanaki 30 kafin ya saka hannu a kudirin ko akasin hakan.

“Ba boyayyen abu ba ne cewa, an aikawa da fadar shugaban kasar da kudurin ne a ranar 31 ga watan Janairun 2022, wanda hakan ke nufin ana da har nan da 1 ga watan Maris kafin a saka hannu.” In ji Adesina.

Ya kara da cewa, “kudurin doka irin wannan da zai yi muhimmin tasiri akan kasar, na bukatar a nutsu a duba shi don a tabbatar ya zama sahihi.”

A cewar Adesina, rashin sanin abin da kundin tsarin mulkin kasa ya kunsa ne ya sa wasu suke ta kurarin da suke yi saboda ba a saka hannu a kudurin dokar ta zabe ba.

Saurarin cikakken rahoton Saleh Shehu Ashaka daga Abuja:

Dokar Zabe: Yadda Kungiyoyin Fararen Hula Suka Yi Zanga-Zanga A Abuja - 2'44"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00

XS
SM
MD
LG