Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dokokin Coronavirus Na Haddasa Zanga-zanga a Amurka


Masu Zanga-zanga a jihar Michigan
Masu Zanga-zanga a jihar Michigan

A wannan mako a jihar Michigan, masu zanga zanga sun taru gaban Majalisar jihar domin bayyana damuwarsu ga dokokin hana zirga zirga.

An gudanar da irin wannan zanga zangar a wurare da dama a Amurka, yayin da wasu mutane ke kalubalantar hakan, abin da suke kallo yafi gwamnati na daukar lokaci wurin kare rayuwar su.

Ruwan sama bai hana masu zanga zangar fitowa gaban Majalisar ba a birnin Lansing na Michigan a jiya Alhamis, domin nuna damuwar su ga dokokin hana zirga zirga na jihar.

Wani mutum a cikin masu zanga zangar ya ce suna da ‘yancin su rayu. Bai yiwuwa a hana su zuwa wurin aiki. ‘Yancin su ne su yi rayuwar su.

Ana samu masu zanga zanga kamar haka a wurare da dama a garuruwa da dama a Amurka. Suna cikin masu matsawa gwamnatocin su lamba a bude ayyuka.

Amma kuma suna zuwa da wasu bukatu, kamar ‘yan mallakar bindiga, kin jinin maganin rigakafi, kin jinin gwamnati amma masoya gwamnatin Trump, wadanda ke amfani da wannan damar domin shigar da bukatun su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG