Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dole Kowa Ya Sa Hannu Don Samun Nasarar Hadin Gwiwa Tsakanin Kasashe


White House
White House

Ba da daɗewa ba bayan Yaƙin Duniya na biyu, ƙasashe masu ƙarfi a duniya sun amince cewa nasarar wasu ƙasashe tana da muhimmanci ga nasu. Don haka, a matsayinsu na mambobin sabuwar Majalisar Dinkin Duniya, sun “amince da wasu ka’idoji don hana rikici da rage radadin dan Adam; don amincewa da kare haƙƙin ɗan adam; don bunkasa tattaunawar da ke gudana don karfafawa da inganta tsarin da nufin amfanar da dukkan mutane, "in ji Sakatariyar Harkokin Wajen Antony Blinken a cikin wani jawabi a gaban Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya a ranar 7 ga Mayu.

Koda yake, "Yanzu, wasu na tambaya ko har yanzu ana iya yin haɗin gwiwa tsakanin bangarorin," in ji Sakatare Blinken. Duk da haka, "hadin gwiwa tsakanin kasashe shi din ne har ila yau mafi alheri wajen tunkarar manyan ƙalubalen duniya."

Amma don tsarin ya cimma, dole ne duk ƙasashe su yi biyayya da shi kuma su sa himma don samun nasararta.

"Akwai hanyoyi uku da za mu iya yin hakan," in ji Sakatare Blinken.

“Na farko, ya kamata dukkan membobin su cika alkawurran da suka dauka - musamman wadanda suka dace da doka.

Hakan ya hada da Yarjejeniyar Majalisar Dinkin Duniya, kudurorin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, dokar jinkai ta kasa da kasa, da dokoki da ka’idojin da aka amince da su a karkashin kulawar Kungiyar Kasuwanci ta Duniya da kungiyoyi da dama na tsara tsarin kasa da kasa. ”

Na biyu, dole haƙƙoƙin ɗan adam da mutuncinsu su kasance a cikin tushen tsarin kasa da kasa.

Na uku, dole ne duk ƙasashe su gane cewa an kafa Majalisar Duniya bisa turbar kiyaye diyaucin kasashen da ke cikin kungiyarda daukarsu a matsayi daya.

Kasa ba ta mutunta wannan ka’idar duk sa’ad da take kokarin sake shata kan iyakokin wani; ko neman warware rikice-rikicen ƙasa ta amfani da ko barazanar ƙarfi; ko lokacin da wata ƙasa ta yi iƙirarin cewa tana da haƙƙin ikon yin tasiri ko tilastawa ga zaɓuka da shawarar wata ƙasa.

Kuma kasa tana nuna raini ga wannan ka’idar lokacin da ta yi bayanai na rashin gaskiya ko cin hanci da rashawa, ta gurgunta zaben wasu kasashen da ke da ‘yanci da adalci da cibiyoyin dimokiradiyya, ko kuma bita da kulli ga ‘yan jarida ko masu adawa da su a kasashen waje. ”

Daga ƙarshe, “bai isa a ce kawai don kare tushen ƙa'idojin da muke da su a yanzu ba. Ya kamata mu inganta kuma mu gini a kai. ”

"A lokacin da aka kafa [Majalisar Dinkin Duniya], [Shugaba Harry a lokacin] Truman ya ce," Wannan Yarjejeniyar ba aikin wata kasa tilo ko wasu kasashe ba ce, ko babba ko karama. Hakan ya samo asali ne daga rushin bayarwa da karbewa, na hakuri da ra'ayi da bukatun wasu, "in ji Sakatare Blinken. "Wannan hujja ce cewa, kasashe za su iya bayyana bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su fuskance su, kuma su sami matsaya guda da za su tsaya a kai."

XS
SM
MD
LG