Accessibility links

Dole Za'a Fara Taron Kasa Goma ga Watan Maris


Shugaba Goodluck Jonathan da Tsohon Shugaba Olusegun Obasanjo. Sun amince da taron kasa kuwa?

Za'a fara taron kasa goma ga watan Maris duk da barazanar kauracewa taron da wasu sassan Najeriya suka yi musamman arewacin kasar.

Goma ga watan Maris ne za'a fara taron kasa kamar yadda gwamnatin tarayyar Najeriya ta shirya.

Duk da nada shugaban taron kasa da sakatarensa da wasu da zasu shugabanci taron har yanzu ana takaddama kan taron musamman a wasu sassan arewa.

Sai dai al'ummomi a arewa maso gabashin kasar na bayyana irin alfanun dake tafe da taron. Sanato Adamu Ajuji Waziri tsohon jakadan Najeriya a kasar Turkiya yace taron da za'a yi akwai abubuwa da yawa da za'a tattauna. Zuwa taron zai fi ma arewa alheri. Yace ya halarci irin wannan tarurukan sau uku har da taron da ya haifarda kundun tsarin mulkin da ake anfani da shi yanzu. Sabili da haka zuwa taron zai yi anfani. Rashin zuwa yana da illa. Yace idan mutum ya je zai ji abun da wasu suke da shi mutum kuma na iya bada amsa. Amma idan mutum bai je ba babu yadda za'a mayarda martani. Yace ko mutum naso ko baya so za'a yi. Yace taron ya shafi kowa da kowa a kasar.

Sanata ya cigaba da cewa yakamata a je domin akwai wasu daga kudancin kasar da suke da ra'ayin a mayarda kasar yankuna shida kuma a raba arzikin kasa kan hakan. Yace to wannan ba zai taimaki arewa ba. Dalili ke nan da yakamata a kasance a wurin taron.

Matasan arewa maso gabas sun ce rashin halartar taron zai cutar dasu. Alhaji Abdulrahaman Kwaccam daya daga cikin shugabannin al'umma na Mubi ta arewa yace idan shugabanninsu basu je ba sun cutar dasu domin dama sun saba cutarsu. Yace sun saba duk abun da ya shafi arewa ba zasu yi ba, ba zasu je ba. Idan kuma sun yi to abu ne wanda ya shafesu ko iyalansu ko kuma za'a taba mulkinsu. Amma duk abun da zai taimaki arewa babu shugabannin arewa da zasu tashi su tabbatar. Yace yau ana kashe 'ya'yan bayin Allah a arewa amma babu shugabanni. Domin haka ya kira matasan arewa da masu ilimi su tabbatar sun bada goyon baya ga taron dari bisa dari.

Ga rahoton Sa'adatu Fawu

XS
SM
MD
LG