WASHINGTON, DC —
Idan kuna biye da mu makon da ya gabata shirin Domin Iyali ya fara haska fitila kan dokar da aka kafa a Karamar Hukumar Gumel ta jihar Jigawa da ta haramta yin kayan aure da su ka wuce kima.
A yau mun gayyaci masu ruwa da tsaki domin nazarin yadda wannan dokar zata amfani al'umma ba tare da tauye hakin wani bangare ba.
Saurari tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.