Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Rahoto Na Musamman Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel, Yuni, 10, 2021


Alheri Grace Abdu

Farkon wannan shekarar majalisar karamar hukumar Gumel a jihar Jigawa ta samar da wani daftarin doka dake haramta yin kayayyakin aure da suke wuce kima. Yayinda wadansu su ke yaba wannan yunkuri da suke gani zai ba mai karamin karfi damar kafa gida, wadansu na ganin an tauye hakkinsu musamman idan aka yi la’akari da wanda yake da karfin yin fiye da abinda dokar ta kayyade.

Saurari rahoto na musamman da Mahmud Ibrahim Kwari ya hada mana:

DOMIN IYALI:Rahoto Na Musamman Kan Dokar Takaita Kayayyakin Aure A Gumel:10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:09:59 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG