Kafin mu yi sallama da bakin da muka gayyata domin tattaunawa kan batun cin zarafi da kuma garkuwa da kananan yara da neman kudin fansa da ake fama da shi, da ya ke kai ga asarar rayuka. A yau, za mu nazarci yadda sakacin magidanta ke jefa al’umma a wannan halin.
Saurari tattaunawar da Madina Dauda ta jagoranta:
-
Grace Alheri Abdu
Grace Alheri Abdu babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.