Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Mata Suna Da Laifi A Rashin Damawa Da Su


Wasu Mata a Lagos cikn shiga irin ta al'adar su suke murnan cika shekaru 55 da samun yancin Najeriya

Bayan hira da manema labarai da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi ranar talatin da watan Disamba da ta gabata, shirin Domin Iyali ya gayyaci wadansu masu fafatukar inganta rayuwar al'umma Mallam Kabiru Dakata, da kuma Maryam Garba Usman domin tattaunawa kan yadda gwamnatin shugaba Buhari zata dama da mata.

Wakilin Sashen Hausa Mahmoud Ibrahim Kwari ya tambayi Mallam Kabiru Dakata abinda yasa duk da jami’an da ake dasu a bangarori da ma’aikatu dabam dabam, da sunan wakiltar iyali, ake ci gaba da samun korafe korafe.

Da yake maida martini, kwamred Dakata yace, ba Magana ce ta wanda suke yi masu wakilci basu yin abinda ya kamata ba, Magana ce ta suma matan a matsa masu su shigo a dama da su, domin idan basu da wakilci a teburin da za a zauna a yanke hukumcin da zai shafe su, kuma ya kasance babu su, babu yadda za a yanke hukumcin da zai gamshe su.

Kabiru Dakata yayi misali da jihar Kano inda ake da ‘yan majalisun jiha guda arba’in babu mace, ko daya, da shugabannin kananan hukumomi fiye da arba’in, babu mace ko daya, da ‘yan majalisun tarayya guda ishirin da hudu, babu mace ko daya. Banda gwamna da mataimaki, yace wannan manuniya ce cewa, har yanzu gwamnatocin Najeriya basu damawa da mata.

Da take bada tata gudummuwar, Maryam Garba Usman tace, mata suna da sha’awar shiga harkokin siyasa da kuma bada gudummuwa a fannin inganta rayuwar al’umma, sai dai galibi ba wadanda suka cancanta, wadanda kuma suke da kwarewa dama.

Ta jadada cewa, mata ne suka fi kusa da ‘ya’yansu sabili da haka sune suka fi dacewa da rike dukan mukaman da suka shafi ci gaban iyali.

Saurari cikakken shirin.

please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:06:37 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG