Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matan 'yansandan da Boko Haram ta kashe sun koka da makalewar hakkokinsu


Wasu matan da 'yan Boko Haram suka kashe mazajensu
Wasu matan da 'yan Boko Haram suka kashe mazajensu

Matan 'yansandan da 'yan kungiyar Boko Haram suka kashe yayinda suka farma barikin 'yansandan a Kano a shekarar 2011 sun koka saboda hukumar 'yansanda bata biyasu hakkokinsu ba.

Mazansu sun mutu sun barsu da yara da dama lokacin da 'yan Boko Haram suka kashesu a shekarar 2011 a barikin 'yansanda a Bompai, Kano, harin da ya rutsa da 'yansanda masu dimbin yawa.

Cikin matan akwai wadda aka barta da yara tara ba tare da samun wani taimako daga koina ba tun 2011.

Bayan rangadi a gidajen matan da suka rasa mazajensu a barikokinsu Hajiya Saliha Muhammad Katsina matar hwamishanan 'yansandan Kano na yanzu ta shirya wani taro da matan domin raba masu kayan masarufin saukaka rayuwa.

Hajiya Saliha tace idan mijin mutum ya mutu akwai wani gurbin da Allah kadai ka iya cikashi. Tace shigowarsu Kano matsalar fyade ya fara daga mata rai amma tace babu yadda za'a ce ta juyawa mata 'yanuwanta baya. Dalili ke nan da ta sa aka tarasu tayi nata gudummawar.

Hajiya Saliha tace tayi magana da mijinta wanda ya yi alkawarin kafa wani kwamiti da zai duba matsalar matan.

Ita ma mataimakiyar hukumar hisba ta Kano mai kula da lamuran mata Malama Zara'u Umar tayi laccan kwantar da hankalin iyayen marayun.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:38 0:00

XS
SM
MD
LG