Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI:Nazari Kan Aure Da Rayuwar Rahama- Kashi Na Biyu- Satumba, 23, 2021


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Idan kuna tare damu makon da ya gabata muka fara tattaunawa da masu ruwa da tsaki kan al’amuran da suka shafi zamantakewar iyali da nufin ganin irin darasin da za a koya daga abinda ya faru da matashiyar da aka yiwa aure tana ‘yar shekaru13 da ya kai ga rasa rai. A yau shirin ya bayyana wadansu daga cikin dalilan da ke kawo sabani tsakanin iyali.

Bakin da muka gayyata a shirin sune, Barista Badiha Abdullahi Mu’az, daya daga cikin lauyoyin da suke kai komo musamman kan al’amuran da suka shafi iyali, da Dr Musa Abdullahi Sufi na gidauniyar A.A Gwarzo dake ayyukan lafiya da jinkan al’umma, sai kuma Mallam Mustapha Mohammed Dandume wanda ke koyarwa kan al’amuran da suka shafi rayuwar Musulmi.

Saurari tattaunawar da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta:

DOMIN IYALI:Nazari Kan Aure Da Rayuwar Rahama- Kashi Na Biyu-10:00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:34 0:00


  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG