Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

DOMIN IYALI: Rawar Da Mata Suka Taka A Zaben Najeriya, Kashi Na Hudu-Afrilu, 20, 2023


Alheri Grace Abdu
Alheri Grace Abdu

Koma bayan da mata suka samu a zabukan da aka gudanar ya maida hannun agogo baya a fafatukar da matan Najeriya ke yi na neman kaso 35 cikin dari na mukaman siyasa da kuma guraban mulki, batun da muka gayyaci masu ruwa da tsaki domin ganin hanyar warware wannan zare.

Har yanzu muna tare da Hon Maryam Umar Kofarmata ‘yar siyasa a jam’iyar APC, da Barrista Amina Umar da ke sharhi kan al’amuran yau da kullum, sai Kwamred Yahaya Shu’aibu Ngogo shima mai sharhi kan al’umuran da suka shafi shugabanci. Kwamred Shu’aibu, na nazarin rawar da mata suka taka a zabukan da aka gudanar a Najeriya da sakamakon ya nuna mata sun sami koma baya lokaci ya kwace mana inda kuma muka dora ke nan a tattaunawa da Mahmud Ibrahim Kwari ya jagoranta.

Saurari cikakken shirin:

DOMIN IYALI: Rawar Da Mata Suka Taka A Zaben Najeriya, Kashi Na Hudu
please wait

No media source currently available

0:00 0:10:15 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

XS
SM
MD
LG